Da Dawuda ya ga fādawansa suna raɗa da juna, sai ya gane lalle yaron ya rasu. Ya tambaye su, ya ce, “Yaron ya rasu ne?”Suka amsa cewa, “I, ya rasu.”