Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 11:12-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai na ce musu, “Idan kun ga daidai ne sai ku biya ni hakkina, idan kuwa ba haka ba ne, to, ku riƙe abinku!” Sai suka biya ni tsabar azurfa talatin, ladana.

13. Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka zuba kuɗin a baitulmalin Haikali.” Sai na ɗauki kuɗin da suka kimanta shi ne tamanina, na zuba su a baitulmalin Haikalin Ubangiji.

14. Sa'an nan kuma na karya sandana na biyun mai suna “Haɗa Kai,” wato alama ke nan da ta nuna na kawar da 'yan'uwancin da yake tsakanin Yahuza da Isra'ila.

15. Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na makiyayi marar amfani.

16. Gama ga shi, zan sa wani makiyayi a ƙasan nan, wanda ba zai kula da masu lalacewa ba, ko waɗanda suka warwatse, ko ya warkar da gurgu, ko ya ciyar da waɗanda suka ragu, amma zai ci naman masu ƙiba, ya farfashe kofatonsu.

17. Taka ta ƙare, kai makiyayi marar amfani,Wanda yakan bar tumakin!Da ma takobi ya sari dantsensa da idonsa na dama!Da ma hannunsa ya shanye sarai,Idonsa na dama kuma ya makance!”

Karanta cikakken babi Zak 11