Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 97:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Jama'ar Sihiyona suna murna,Garuruwan Yahuza kuma suna farin ciki,Sabili da irin shari'unka, ya Ubangiji!

9. Ya Ubangiji Mai Iko Dukka, kai kake mulkin dukan duniya,Ka fi sauran alloli duka girma.

10. Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta.Yakan kiyaye rayukan jama'arsa,Yakan cece su daga ikon mugaye.

11. Haske yakan haskaka adalai,Haka kuma murna ta cika ga masu nagarta.

12. Dukanku adalai ku yi murna,Saboda abin da Ubangiji ya yi!Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya yi,Ku yi masa godiya!

Karanta cikakken babi Zab 97