Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 96:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka,Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.

9. Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa'ad da ya bayyana,Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka!

10. A faɗa wa dukan sauran al'umma, “Ubangiji Sarki ne!Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta,Ba za a iya kaushe ta ba,Shi zai shara'anta dukan jama'a da adalci.”

11. Duniya da sararin sama, ku yi murna!Ki yi ruri, ya ke teku da dukan masu rai da suke cikinki,

12. Ku yi murna ya ku filaye da dukan abubuwan da suke cikinku!Sa'an nan itatuwan da suke cikin kuramaZa su ta da murya saboda farin ciki

Karanta cikakken babi Zab 96