Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 95:8-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.

9. A can suka gwada ni suka jarraba ni,Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.

10. A shekara arba'in ɗin nan,Jama'ar nan ta zama abar ƙyama gare ni,‘Su marasa biyayya ne,’ in ji ni,‘Gama sun ƙi bin umarnaina!’

11. Sai na ji haushi, na yi musu alkawari mai nauyi.Na ce, ‘Faufau ba za ku shiga ƙasar da zan ba ku hutawa a ciki ba.’ ”

Karanta cikakken babi Zab 95