Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 95:7-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Shi ne Allahnmu,Mu ne jama'ar da yake lura da ita,Mu ne kuma garken da yake ciyarwa.Yau ku ji abin da yake faɗa.

8. “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.

9. A can suka gwada ni suka jarraba ni,Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.

10. A shekara arba'in ɗin nan,Jama'ar nan ta zama abar ƙyama gare ni,‘Su marasa biyayya ne,’ in ji ni,‘Gama sun ƙi bin umarnaina!’

Karanta cikakken babi Zab 95