Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 95:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku zo mu yabi Ubangiji!Mu raira waƙa domin farin ciki ga mai kiyaye mu,Da Mai Cetonmu!

2. Mu zo gabansa da godiya,Mu raira waƙoƙin farin ciki na yabo!

3. Gama Ubangiji Allah ne mai iko,Shi yake mulki bisa sauran alloli duka.

4. Yana mulki bisa dukan duniya,Daga zurfafan kogwannin duwatsu zuwa tuddai mafiya tsayi.

5. Yana mulki bisa tekun da ya yi,Da kuma bisa ƙasar da ya siffata.

6. Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada,Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!

7. Shi ne Allahnmu,Mu ne jama'ar da yake lura da ita,Mu ne kuma garken da yake ciyarwa.Yau ku ji abin da yake faɗa.

8. “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.

Karanta cikakken babi Zab 95