Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 95:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku zo mu yabi Ubangiji!Mu raira waƙa domin farin ciki ga mai kiyaye mu,Da Mai Cetonmu!

2. Mu zo gabansa da godiya,Mu raira waƙoƙin farin ciki na yabo!

3. Gama Ubangiji Allah ne mai iko,Shi yake mulki bisa sauran alloli duka.

4. Yana mulki bisa dukan duniya,Daga zurfafan kogwannin duwatsu zuwa tuddai mafiya tsayi.

Karanta cikakken babi Zab 95