Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 94:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Na ce, “Ina kan fāɗuwa,”Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.

19. Sa'ad da nake alhini, ina cikin damuwa,Ka ta'azantar da ni, ka sa in yi murna.

20. Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya,Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu,

21. Sukan shirya wa mutanen kirki maƙarƙashiya,Sukan yanke wa marar laifi hukuncin kisa.

22. Amma Ubangiji yakan kāre ni,Allahna yakan kiyaye ni.

23. Shi zai hukunta su saboda muguntarsu,Ya hallaka su saboda zunubansu.Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.

Karanta cikakken babi Zab 94