Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 91:5-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ba za ka ji tsoron hatsarori da dare ba,Ko fāɗawar da za a yi maka da rana,

6. Ko annobar da take aukowa da dare,Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.

7. Mutum dubu za su fāɗi daura da kai,Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai,Amma kai, ba za a cuce ka ba.

8. Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.

9. Domin ka ɗauka Ubangiji yake kiyaye ka,Maɗaukaki ne yake tsaronka,

10. To, ba bala'in da zai same ka,Ba za a yi wa gidanka aikin ƙarfi da yaji ba.

11. Allah zai sa mala'ikunsa su lura da kai,Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi.

12. Za su ɗauke ka a hannuwansu,Don kada ka buga ƙafarka a dutse.

13. Za ka tattake zakoki da macizai,Za ka tattake zakoki masu zafin raiDa macizai masu dafi.

14. Allah ya ce, “Zan ceci waɗanda suke ƙaunata,Zan kiyaye waɗanda suka san ni.

15. Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu,Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala,Zan cece su in girmama su.

Karanta cikakken babi Zab 91