Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 91:12-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Za su ɗauke ka a hannuwansu,Don kada ka buga ƙafarka a dutse.

13. Za ka tattake zakoki da macizai,Za ka tattake zakoki masu zafin raiDa macizai masu dafi.

14. Allah ya ce, “Zan ceci waɗanda suke ƙaunata,Zan kiyaye waɗanda suka san ni.

15. Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu,Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala,Zan cece su in girmama su.

16. Zan ba su tsawon rai lada,Hakika kuwa zan cece su.”

Karanta cikakken babi Zab 91