Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 90:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba'in,In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne.Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaruSuke kawo mana, damuwa ce da wahala,Nan da nan sukan wuce,Tamu da ƙare.

11. Wa ya san iyakar ikon fushinka?Wa ya san irin tsoron da hasalarka za ta kawo?

12. Ka koya mana mu sani ranmu na ɗan lokaci ne,Domin mu zama masu hikima.

13. Ya Ubangiji, sai yaushe za ka ji tausayinmu?Ka ji tausayin bayinka!

14. Ka cika mu da madawwamiyar ƙaunarka a kowace safiya,Don mu raira waƙoƙin murna dukan kwanakin ranmu.

15. Yanzu sai ka sa mu yi farin ciki mai yawa,Kamar yadda ka sa muka yi baƙin cikiA dukan shekarun nan, da muka sha wahala.

16. Ka yarda mana, mu bayinka, mu ga ayyukanka masu girma,Ka yardar wa zuriyarmu su ga ikonka mai girma.

17. Ka yarda, albarkarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji Allahnmu.Ka sa mu yi nasara game da dukan abin da za mu yi!I, ka ba mu nasara a dukan abin da muke yi!

Karanta cikakken babi Zab 90