Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 9:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji,Zan hurta dukan abubuwa masu banmamaki da ka yi.

2. Zan raira waƙa da farin ciki sabili da kai,Zan raira yabo gare ka, ya Maɗaukaki!

3. Magabtana sun jā da baya da suka gan ka,Suka faɗi, suka mutu.

4. Kai da kake alƙali mai adalciKa zauna a kursiyinka,Ka kuwa yi shari'ar da ta yi mini daidai.

5. Ka kā da arna,Ka kuma hallakar da mugaye,Ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba.

6. An hallaka abokan gābanmu har abada,Ka lalatar da biranensu,An kuma manta da su sarai.

7. Amma Ubangiji sarki ne har abada,Ya kafa kursiyinsa domin yin shari'a.

8. Yana mulkin duniya da adalci,Yana yi wa mutane shari'a da gaskiya.

Karanta cikakken babi Zab 9