Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 88:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Kakan yi wa matattu mu'ujizai ne?Sukan tashi su yabe ka?

11. Akan yi maganar madawwamiyar ƙaunarka a kabari?Ko amincinka a inda ake hallaka?

12. Za a iya ganin mu'ujizanka a cikin duhu?Ko kuwa alherinka a lahira?

13. Ya Ubangiji, ina kira gare ka, neman taimako,Kowace safiya nakan yi addu'a gare ka.

14. Me ya sa ka yashe ni, ya Ubangiji?Me ya sa ka ɓoye kanka daga gare ni?

15. Tun ina ƙarami nake shan wahala,Har ma na kusa mutuwa,Na tafke saboda nauyin hukuncinka.

16. Hasalarka ta bi ta kaina,Tasar mini da kake ta yi, ta hallaka ni.

17. Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa,Ta kowace fuska, sun rufe ni.

18. Ka sa har abokaina na kusa sun yashe ni,Duhu ne kaɗai abokin zamana.

Karanta cikakken babi Zab 88