Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 88:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji Allah, Mai Cetona,Duk yini ina ta kuka,Da dare kuma na zo gare ka.

2. Ka ji addu'ata,Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako!

3. Wahala mai yawa ta auko mini,Har ina gab da mutuwa.

4. Ina daidai da sauran mutanen da suke gab da mutuwa,Dukan ƙarfina ya ƙare.

5. An yashe ni a cikin matattu,Kamar waɗanda aka karkashe,Suna kuma kwance cikin kaburburansu,Waɗanda ka manta da su ɗungum,Waɗanda taimakonka ya yi musu nisa.

6. Ka jefar da ni cikin zurfin kabari,Da cikin rami mafi zurfi, mafi duhu.

7. Fushinka yana da nauyi a kaina,An turmushe ni a cikin tuƙuƙinka.

8. Ka sa abokaina su yashe ni,Ka sa sun ware ni.An kange ni, ba yadda zan kuɓuta.

9. Idanuna sun raunana saboda wahala.Ya Ubangiji, kowace rana ina kira gare ka,Ina ta da hannuwana zuwa gare ka da addu'a!

10. Kakan yi wa matattu mu'ujizai ne?Sukan tashi su yabe ka?

11. Akan yi maganar madawwamiyar ƙaunarka a kabari?Ko amincinka a inda ake hallaka?

Karanta cikakken babi Zab 88