Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 86:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kai ne Allahna, saboda haka ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,Ina yin addu'a a gare ka dukan yini.

4. Ka sa bawanka yă yi murna, ya Ubangiji,Saboda addu'o'ina sun hau zuwa gare ka.

5. Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara,Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.

6. Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka ji kukana na neman taimako!

7. Nakan kira gare ka a lokacin wahala,Saboda kakan amsa addu'ata.

8. Ba wani allah kamarka, ya Ubangiji,Ba ko ɗaya, ba wanda zai iya aikata abin da kake aikatawa.

9. Dukan sauran al'umma da ka halittaZa su zo su rusuna har ƙasa a gabanka.Za su yabi girmanka,

10. Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah,Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.

11. Ya Ubangiji, ka koya mini abin da kake so in yi,Ni kuwa zan yi maka biyayya da aminci.Ka koya mini in bauta maka da zuciya ɗaya.

12. Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji Allahna,Zan riƙa shelar girmanka har abada.

13. Wane irin girma madawwamiyar ƙaunarka take da shi a gare ni!Gama ka cece ni daga zurfin kabari.

14. Masu girmankai sun tasar mini, ya Allah,Ƙungiyar mugaye tana ƙoƙari ta kashe ni,Mutanen da ba su kula da kai ba.

15. Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna,Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.

Karanta cikakken babi Zab 86