Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 86:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka kasa kunne gare ni, ya Ubangiji, ka amsa mini,Gama ba ni da ƙarfi, ba ni kuwa da mataimaki.

2. Ka cece ni daga mutuwa, saboda ni mai aminci ne a gare ka,Ka cece ni saboda ni bawanka ne, ina kuwa dogara gare ka.

3. Kai ne Allahna, saboda haka ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,Ina yin addu'a a gare ka dukan yini.

4. Ka sa bawanka yă yi murna, ya Ubangiji,Saboda addu'o'ina sun hau zuwa gare ka.

5. Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara,Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.

6. Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka ji kukana na neman taimako!

7. Nakan kira gare ka a lokacin wahala,Saboda kakan amsa addu'ata.

8. Ba wani allah kamarka, ya Ubangiji,Ba ko ɗaya, ba wanda zai iya aikata abin da kake aikatawa.

9. Dukan sauran al'umma da ka halittaZa su zo su rusuna har ƙasa a gabanka.Za su yabi girmanka,

10. Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah,Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.

Karanta cikakken babi Zab 86