Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 85:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ka daina yin fushi da su,Ka kuwa kawar da zafin fushinka.

4. Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu,Ka daina jin haushinmu!

5. Za ka yi fushi da mu har abada?Ba za ka taɓa hucewa ba?

6. Ka daɗa mana ƙarfi, ka yarda ka sabunta ƙarfinmu,Mu kuwa, jama'arka, za mu yabe ka.

7. Ka ƙaunace mu da madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,Ka taimake mu da cetonka.

8. Ina kasa kunne ga abin da Ubangiji Allah yake cewa,Mu da muke mutanensa, ya alkawarta mana salama,Idan ba mu koma kan al'amuranmu na wauta ba.

Karanta cikakken babi Zab 85