Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 85:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, ka yi wa ƙasarka alheri,Ka sāke arzuta Isra'ila kuma.

2. Ka gafarta wa jama'arka zunubansu,Ka kuwa gafarta musu dukan kuskurensu,

3. Ka daina yin fushi da su,Ka kuwa kawar da zafin fushinka.

4. Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu,Ka daina jin haushinmu!

5. Za ka yi fushi da mu har abada?Ba za ka taɓa hucewa ba?

Karanta cikakken babi Zab 85