Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 83:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ya Allahna, ka warwatsa su kamar ƙura,Ka warwatsa su kamar ciyayin da iska take hurawa.

14. Kamar yadda wuta take cin jeji,Kamar yadda harshen wuta yake ƙone tuddai,

15. Ka runtume su da hadirinka,Ka razanar da su da iskarka mai ƙarfi.

16. Ya Ubangiji, ka sa kunya ta rufe su,Don su so su bauta maka.

17. Ka sa a kore su, a razanar da su har abada,Ka sa su mutu, mutuwar ƙasƙanci!

18. Ka sa su sani kai kaɗai ne Ubangiji,Kai kaɗai ne mamallakin dukan duniya!

Karanta cikakken babi Zab 83