Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 83:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Allah, kada ka yi shiru,Kada ka tsaya cik,Ya Allah, kada kuma ka yi tsit!

2. Duba, abokan gābanka suna tawaye,Maƙiyanka sun tayar.

3. Suna ta ƙulle-ƙulle a asirce gaba da jama'arka,Suna shirya maƙarƙashiya gāba da waɗanda kake tsaronsu.

4. Suna cewa, “Ku zo, mu hallakar da al'ummarsu,Don a manta da Isra'ila har abada!”

5. Suka yarda a kan abin da suka shirya,Suka haɗa kai gāba da kai.

6. Su ne mutanen Edom, da Isma'ilawa,Da mutanen Mowab, da Hagarawa,

7. Da mutanen Gebal, da na Ammon, da na Amalek,Da na Filistiya, da na Taya.

8. Assuriya ma ta haɗa kai da su,Haɗa kai ke nan mai ƙarfi da zuriyar Lutu.

9. Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa,Ka yi musu yadda ka yi wa SiseraDa Yabin a Kogin Kishon,

Karanta cikakken babi Zab 83