Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 81:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu,Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu!

2. A fara waƙa, ku buga bandiri,Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.

3. Ku busa ƙaho domin idin,A amaryar wata,Da a tsakiyar farin wata.

4. Wannan doka ce a Isra'ila,Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu.

5. Ya ba da wannan umarni ga jama'ar Isra'ila,A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar.Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa,

Karanta cikakken babi Zab 81