Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 80:7-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ka komo da mu, ya Allah Mai Runduna!Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!

8. Ka fito da kurangar inabi daga cikin Masar,Ka kori sauran al'umma,Ka dasa kurangar a ƙasarsu.

9. Ka gyara mata wuri don ta yi girma,Saiwoyinta suka shiga ƙasa sosai,Ta yaɗu, ta rufe dukan ƙasar.

10. Ta rufe tuddai da inuwarta,Ta rufe manya manyan itatuwan al'ul da rassanta.

11. Rassanta sun miƙe har Bahar Rum,Har zuwa Kogin Yufiretis.

12. Me ya sa ka rushe shingen da yake kewaye da ita?Ga shi yanzu, duk mai wucewa yana iya satar 'ya'yanta.

Karanta cikakken babi Zab 80