Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 80:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ka ciyar da mu da hawaye,Ka shayar da mu da babban ƙoƙo na hawaye.

6. Ka bar al'umman da take makwabtaka da muSu yi ta faɗa a kan ƙasarmu,Abokan gābanmu kuma suna yi mana ba'a.

7. Ka komo da mu, ya Allah Mai Runduna!Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!

8. Ka fito da kurangar inabi daga cikin Masar,Ka kori sauran al'umma,Ka dasa kurangar a ƙasarsu.

9. Ka gyara mata wuri don ta yi girma,Saiwoyinta suka shiga ƙasa sosai,Ta yaɗu, ta rufe dukan ƙasar.

10. Ta rufe tuddai da inuwarta,Ta rufe manya manyan itatuwan al'ul da rassanta.

Karanta cikakken babi Zab 80