Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 80:14-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ka juyo wurinmu, ya Allah Mai Runduna!Daga Sama, ka dube mu,Ka zo ka ceci kurangar inabinka!

15. Ka zo ka ceci kurangar inabin nanWadda kai da kanka ka dasa,Wannan ƙaramar kuranga,Ka sa ta yi girma, ta yi ƙarfi sosai!

16. Abokan gābanmu sun sa mata wuta, sun sare ta,Ka yi fushi da su, ka hallaka su!

17. Ka kiyaye jama'arka wadda ka zaɓa,Ka keɓe ta.Al'umman nan wadda ka sa ta yi girma, ta yi ƙarfi sosai!

18. Ba za mu ƙara rabuwa da kai ba,Ka rayar da mu, mu kuwa za mu yabe ka.

19. Ka komo da mu, ya Ubangiji Allah Mai Runduna!Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!

Karanta cikakken babi Zab 80