Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 79:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Don me al'ummai za su tambaye mu cewa,“Ina Allahnku?”Bari mu ga ka hukunta al'ummaiSaboda sun zubar da jinin bayinka!

11. Ka kasa kunne ga nishin 'yan sarƙa,Ka kuɓutar da waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa,Ta wurin ikonka mai girma.

12. Ya Ubangiji, ka rama wa al'umman nan har sau bakwai,Saboda tsiwace-tsiwacen da suka yi maka.

13. Mu waɗanda muke jama'arka, tumakin garkenka,Za mu gode maka, mu yabe ka har abada.

Karanta cikakken babi Zab 79