Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 79:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Allah, arna sun fāɗa wa ƙasar jama'arka!Sun ƙazantar da Haikalinka tsattsarka,Sun bar Urushalima kufai.

2. Suka bar wa tsuntsaye gawawwakin jama'arka su ci,Suka bar wa namomin jeji gawawwakin bayinka.

3. Suka zubar da jinin jama'arka kamar ruwa,Jini ya yi ta gudu kamar ruwaKo'ina a Urushalima,Ba ma wanda ya ragu don yă binne gawawwaki.

4. Sauran al'ummar da take kewaye da mu,Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya,Suka yi mana ba'a.

5. Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji?Har abada ne?Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta?

6. Ka yi fushi da al'umman da ba su yi maka sujada,Ka yi fushi da jama'ar da suka ƙi ka!

7. Sun karkashe mutanenmu,Sun kuwa lalatar da ƙasarmu.

8. Kada ka hukunta mu saboda zunuban kakanninmu,Amma ka yi mana jinƙai yanzu,Gama mun fid da zuciya sarai.

Karanta cikakken babi Zab 79