Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:4-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ba za mu ɓoye waɗannan abubuwa daga 'ya'yanmu ba,Amma za mu faɗa wa tsara mai zuwaLabarin ikon Ubangiji, da manya manyan ayyukansa,Da abubuwan banmamaki waɗanda ya aikata.

5. Ya ba da dokoki ga jama'ar Isra'ila,Da umarnai ga zuriyar Yakubu.Ya ba kakanninmu ka'idodi,Don su koya wa 'ya'yansu dokokinsa,

6. Saboda tsara mai zuwa ta koye su,Su kuma su koya wa 'ya'yansu.

7. Ta haka su ma za su dogara ga Allah,Ba za su manta da abin da ya yi ba,Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.

8. Kada su zama kamar kakanninsu,Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya.Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba,Ba su kuwa yi masa aminci ba.

9. Ifraimawa waɗanda suka yi yaƙi da bakkuna da kibauSuka gudu a ranar yaƙi.

10. Ba su kiyaye alkawarinsu da Allah ba,Sun ƙi biyayya da dokokinsa.

11. Sun manta da abin da ya aikata,Da mu'ujizan nan da ya nuna musu.

12. Kakanninsu na kallo sa'ad da Allah ya aikata wata mu'ujizaA filin Zowan a ƙasar Masar.

13. Ya raba teku, ya ratsa da su ta cikinta,Ya sa ruwa ya tsaya kamar bango.

14. Da rana sai ya bi da su da girgije,Da dare kuwa ya bi da su da hasken wuta.

15. Ya tsaga duwatsu, suka buɗe a hamada,Ya ba su ruwa daga cikin zurfafa.

16. Ya sa rafi ya fito daga cikin dutse,Ya sa ruwan ya yi gudu kamar a kogi.

17. Amma sun ci gaba da yi wa Allah zunubi,A hamada suka yi wa Maɗaukaki tawaye.

18. Da gangan suka jarraba Allah,Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.

19. Suka yi magana gāba da Allah, suka ce,“Ko Allah yana da iko ya ba mu abinci a hamada?

20. Gaskiya ce, ya bugi dutse,Ruwa kuwa ya fito a yalwace,Amma ko yana da iko ya ba da abinci da nama ga jama'arsa?”

21. Saboda haka Allah ya yi fushi sa'ad da ya ji su,Ya aukar wa jama'arsa da wuta,Fushinsa ya haɓaka a kansu,

22. Saboda ba su amince da shi ba,Ba su kuma gaskata yana da ikon cetonsu ba.

Karanta cikakken babi Zab 78