Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku kasa kunne ga koyarwata, ya ku jama'ata,Ku kula da abin da nake faɗa.

2. Zan yi magana da ku,In faɗa muku asirai na dā,

3. Abubuwan da muka ji muka kuwa sani,Waɗanda kakanninmu suka faɗa mana.

4. Ba za mu ɓoye waɗannan abubuwa daga 'ya'yanmu ba,Amma za mu faɗa wa tsara mai zuwaLabarin ikon Ubangiji, da manya manyan ayyukansa,Da abubuwan banmamaki waɗanda ya aikata.

5. Ya ba da dokoki ga jama'ar Isra'ila,Da umarnai ga zuriyar Yakubu.Ya ba kakanninmu ka'idodi,Don su koya wa 'ya'yansu dokokinsa,

6. Saboda tsara mai zuwa ta koye su,Su kuma su koya wa 'ya'yansu.

7. Ta haka su ma za su dogara ga Allah,Ba za su manta da abin da ya yi ba,Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.

8. Kada su zama kamar kakanninsu,Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya.Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba,Ba su kuwa yi masa aminci ba.

Karanta cikakken babi Zab 78