Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 77:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na ta da murya, na yi kuka ga Allah,Na ta da murya, na yi kuka, ya kuwa ji ni.

2. A lokacin wahala, nakan yi addu'a ga Ubangiji,Dukan dare nakan ɗaga hannuwana sama in yi addu'a,Amma ban sami ta'aziyya ba.

3. Lokacin da na tuna da Allah na yi ajiyar zuciya.Sa'ad da nake tunani,Nakan ji kamar in fid da zuciya.

4. Ba ya barina in yi barci,Na damu har na kāsa magana.

5. Na yi tunanin kwanakin da suka wuce,Nakan kuma tuna da shekarun da suka wuce da daɗewa.

Karanta cikakken babi Zab 77