Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 74:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sun sa wa Haikalinka wuta,Sun ƙazantar da wurin da akan yi maka sujada,Sun farfashe shi duk.

8. Sun yi niyya su murƙushe mu sarai,Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.

9. Ba sauran tsarkakan alamu,Ba sauran annabawan da suka ragu,Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.

10. Ya Allah, har yaushe abokan gābanmu za su yi ta yi mana ba'a?Za su yi ta zargin sunanka har abada ne?

11. Me ya sa ka ƙi taimakonmu?Ka tasar musu ka hallaka su!

12. Amma ya Allah, kai ne Sarkinmu tun daga farko,Ka yi nasara da duniya.

13. Da ƙarfin ikonka ka raba teku,Ka farfashe kawunan dodannin ruwa,

14. Ka ragargaje kawunan kadduna,Ka kuwa ba mutanen hamada su ci.

15. Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu,Ka sa manyan koguna su ƙafe.

16. Ka halicci yini da dare,Ka sa rana da wata a wurarensu.

17. Ka yi wa duniya kan iyaka,Ka kuwa yi lokatan damuna da na rani.

Karanta cikakken babi Zab 74