Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 74:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ya Allah, har yaushe abokan gābanmu za su yi ta yi mana ba'a?Za su yi ta zargin sunanka har abada ne?

11. Me ya sa ka ƙi taimakonmu?Ka tasar musu ka hallaka su!

12. Amma ya Allah, kai ne Sarkinmu tun daga farko,Ka yi nasara da duniya.

13. Da ƙarfin ikonka ka raba teku,Ka farfashe kawunan dodannin ruwa,

14. Ka ragargaje kawunan kadduna,Ka kuwa ba mutanen hamada su ci.

15. Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu,Ka sa manyan koguna su ƙafe.

16. Ka halicci yini da dare,Ka sa rana da wata a wurarensu.

17. Ka yi wa duniya kan iyaka,Ka kuwa yi lokatan damuna da na rani.

18. Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a,Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.

19. Kada ka ba da jama'arka marasa taimakoA hannun mugayen maƙiyansu,Kada ka manta da jama'arka waɗanda ake tsananta musu!

20. Ka tuna da alkawarin da ka yi mana,Akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar!

21. Kada ka bari a kori waɗanda ake zalunta,Amma bari matalauta da masu mayata su yabe ka.

22. Ka tashi, ya Allah, ka kāre kanka!Ka tuna fa, marasa tsoronka suna ta yi maka ba'a dukan yini!

23. Kada ka manta da hargowar maƙiyanka,Kada ka manta da hayaniyar da magabtanka suke ta yi.

Karanta cikakken babi Zab 74