Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 72:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka koya wa sarki ya yi shari'aDa adalcinka, ya Allah,Ka kuma ba shi shari'arka,

2. Don ya yi mulkin jama'arka bisa kan shari'a,Ya kuma bi da mulki da adalci.

3. Ka sa ƙasar ta mori wadatarta,Ka sa al'ummar ta san adalci.

4. Ka sa sarki ya yi wa talakawa shari'ar gaskiya,Ya taimaki waɗanda suke da bukata,Ya kuma hukunta azzalumai!

5. Ka sa su girmama kaMuddin rana tana haskakawa,Muddin wata yana ba da haske dukan lokaci.

6. Ka sa sarki ya zama kamar ruwan sama a gonaki,Ya zama kamar yayyafi a bisa ƙasa.

7. Ka sa adalci ya bunƙasa a zamaninsa,Wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa.

Karanta cikakken babi Zab 72