Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 68:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da ma Allah ya tashi ya warwatsa maƙiyansa!Da ma su waɗanda suke ƙinsa su gudu!

2. Kamar yadda iska take korar hayaƙi,Haka nan zai kore su,Kamar yadda kākin zuma yakan narke a gaban wuta,Haka nan mugaye za su hallaka a gaban Allah.

3. Amma adalai za su yi murna,Su kuma yi farin ciki a gaban Allah,Za su yi murna ƙwarai da gaske.

4. Ku raira waƙa ga Allah,Ku raira waƙar yabo ga sunansa,Ku yi hanya ga wanda yake ratsa gizagizai.Sunansa kuwa Ubangiji ne, ku yi murna a gabansa!

5. Allah, wanda yake zaune a tsattsarkan Haikalinsa,Yana lura da marayu, yana kuwa kiyaye gwauraye,Wato matan da mazansu suka mutu.

6. Yakan ba waɗanda suke da kewa gida, su zauna a ciki,Yakan fitar da 'yan sarƙa ya kai su 'yanci mai daɗi,Amma 'yan tawaye za su zauna a ƙasar da ba kowa a ciki.

7. Sa'ad da ka bi da jama'arka, ya Allah,Sa'ad da ka yi tafiya a hamada,

8. Duniya ta girgiza, sararin sama ya kwararo ruwa,Saboda bayyanar Allah, har Dutsen Sinai ya girgiza,Saboda bayyanar Allah na Isra'ila.

9. Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah,Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.

10. Jama'arka suka gina gidajensu a can,Ta wurin alherinka ka yi wa matalauta tanadi.

11. Ubangiji ya ba da umarni,Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,

12. “Sarakuna da rundunan sojojinsu suna gudu!Matan da suke a gida suka rarraba ganima.”

Karanta cikakken babi Zab 68