Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 66:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ka jarraba mu, ya Allah,Kamar yadda ake tace azurfa da wuta,Haka nan ka jarraba mu.

11. Ka bar mu muka fāɗa a tarko,Ka ɗora mana kaya masu nauyi.

12. Ka bar maƙiyanmu suka tattaka mu,Mun ratsa ta cikin wuta da rigyawa,Amma yanzu ka kawo mu a lafiyayyen wuri.

13. Zan kawo hadayun ƙonawa a ɗakinka,Zan miƙa maka abin da na alkawarta.

14. Zan ba ka abin da na ce zan bayar,A lokacin da nake shan wahala.

15. Zan miƙa tumaki don a ƙona a kan bagade,Nan za a ji ƙanshi mai daɗi na ƙonannun awaki,Zan miƙa hadayu na bijimai da na awaki.

16. Ku zo ku ji, dukanku, ku da kuke girmama Allah,Ni kuwa zan faɗa muku abin da ya yi mini.

17. Na yi kira gare shi neman taimako,A shirye nake in yabe shi da waƙoƙi.

18. Da ban watsar da zunubaina ba,Da Ubangiji bai ji ni ba.

19. Amma hakika Allah ya ji ni,Ya saurari addu'ata.

20. Ina yabon Allah,Domin bai ƙi addu'ata ba,Bai kuwa hana mini madawwamiyar ƙaunarsa ba.

Karanta cikakken babi Zab 66