Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 63:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Allah, kai ne Allahna,Ina sa zuciya gare ka.Duk niyyata ta nemanka ce,Raina yana ƙishinka,Kamar bussasshiyar ƙasa,Wadda ta zozaye, ba ta da ruwa.

2. Bari in gan ka a tsattsarkan wurinka,In dubi ɗaukakarka da darajarka.

3. Madawwamiyar ƙaunarka ta fi rai kansa,Saboda wannan zan yabe ka.

4. Muddin raina, zan yi maka godiya,Zan ta da hannuwana sama, in yi addu'a gare ka.

5. Raina zai yi liyafa, yă ƙoshi sosai,Ni kuwa zan raira waƙoƙin murna na yabo a gare ka.

6. Sa'ad da nake kwance a gadona na tuna da kai,Dare farai ina ta tunawa da kai,

7. Domin kai kake taimakona kullayaumin.Da murna, nake raira waƙa,A inuwar fikafikanka,

8. Raina yana manne maka,Ikonka yana riƙe da ni.

Karanta cikakken babi Zab 63