Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 6:7-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka,Har da ƙyar nake iya gani,Duk kuwa saboda abokan gābana!

8. Ku tafi daga nan, ku masu aikin mugunta!Ubangiji yana jin kukana.

9. Yana kasa kunne ga kukana na neman taimako,Yana kuwa amsa addu'o'ina.

10. Abokan gābana duka za su sha kunyar fāɗuwarsu,Suna cikin matsanancin ruɗami,Za a kwashe su farat ɗaya.

Karanta cikakken babi Zab 6