Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 59:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka cece ni daga maƙiyana, ya Allahna,Ka kiyaye ni daga waɗanda suka tasar mini!

2. Ka cece ni daga waɗannan mugaye,Ka tsirar da ni daga masu kisankan nan!

3. Duba! Suna jira su auka mini,Mugaye suna taruwa gāba da ni,Ba domin wani zunubi ko wani laifin da na yi ba,

4. Ba domin na yi wani laifi ba, ya Ubangiji,Har da suka gaggauta gāba da ni.Kai da kanka ka gani, ya Allah na Isra'ila!Ka tashi ka taimake ni.

5. Ka tashi, ya Ubangiji, Allah Maɗaukaki, ka taimake ni,Ka tashi ka hukunta al'ummai,Kada ka yi wa waɗannan mugaye, maciya amana, jinƙai!

Karanta cikakken babi Zab 59