Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 53:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Allah ya ce, “Ashe, ba su sani ba?Ashe, mugayen nan jahilai ne?Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke rayuwa,Ba sa yin addu'a gare ni.”

5. Amma sa'an nan za su firgita ƙwarai,Irin yadda ba su taɓa yi ba,Gama Allah ya warwatsa ƙasusuwan maƙiyanka.Ya kore su sarai, saboda ya ƙi su.

6. Dā ma ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona!Sa'ad da Allah ya sāke arzuta jama'arsa,Zuriyar Yakubu za ta yi farin ciki,Jama'ar Isra'ila kuwa za ta yi murna.

Karanta cikakken babi Zab 53