Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 50:7-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Ku ji, ya ku jama'ata, zan kuwa yi magana,Zan ba da shaida gāba da ku, ya Isra'ila.Ni ne Allah, Allahnku.

8. Ban tsauta muku saboda hadayunku ba,Ko saboda hadayu na ƙonawa da kuke ta miƙa mini kullum.

9. Ba na bukatar bijimai daga gonakinku,Ko awaki daga garkunanku.

10. Gama namomin jeji nawa ne,Dubban shanu da suke kan tuddai kuma nawa ne.

11. Dukan tsuntsayen da suke tashi a sararin sama nawa ne,Da dukan masu rai da suke ƙasa.

12. “Da ina jin yunwa ba sai na faɗa muku ba,Gama da duniya da dukan abin da yake cikinta nawa ne.

13. Nakan ci naman bijimai ne?Ko nakan sha jinin awaki?

14. Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya,Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.

15. Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo,Zan cece ku,Ku kuwa za ku yabe ni.”

16. Amma Allah ya ce wa mugaye,“Don me za ku haddace umarnaina?Don me za ku yi magana a kan alkawaraina?

17. Kun ƙi in tsauta muku,Kun yi watsi da umarnaina.

18. Sa'ad da kuka ga ɓarawo kukan yi abuta da shi.Kuna haɗa kai da mazinata.

Karanta cikakken babi Zab 50