Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 50:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah Maɗaukaki, Ubangiji, ya yi magana,Yana kiran dukan duniya, daga gabas zuwa yamma.

2. Allah yana haskakawa daga Sihiyona,Da cikar jamalin Sihiyona.

3. Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba,Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa,Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.

4. Ya kira sammai da duniya su zama shaidu,Su ga yadda yake shara'anta jama'arsa.

5. Ya ce, “Ku tattaro mini amintattuna,Waɗanda suka cika alkawarin da yake tsakanina da su,Ta wurin miƙa hadaya.”

6. Sammai suna shelar adalcin Allah,Domin shi yake yin shari'a!

7. “Ku ji, ya ku jama'ata, zan kuwa yi magana,Zan ba da shaida gāba da ku, ya Isra'ila.Ni ne Allah, Allahnku.

8. Ban tsauta muku saboda hadayunku ba,Ko saboda hadayu na ƙonawa da kuke ta miƙa mini kullum.

9. Ba na bukatar bijimai daga gonakinku,Ko awaki daga garkunanku.

10. Gama namomin jeji nawa ne,Dubban shanu da suke kan tuddai kuma nawa ne.

Karanta cikakken babi Zab 50