Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 45:13-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Gimbiya tana fāda, kyakkyawa ce ainun,Da zaren zinariya aka saƙa rigarta,

14. Aka kai ta wurin sarki tana saye da riga mai ado.Ga 'yan matanta a biye,Aka kawo su wurin sarki.

15. Da farin ciki da murna suka zo,Suka shiga fādar sarki.

16. Za ka haifi 'ya'ya maza da yawa,Waɗanda za su maye matsayin kakanninka,Za ka sa su zama masu mulkin duniya duka.

17. Waƙata za ta sa a yi ta tunawa da sunanka har abada,Dukan jama'a za su yabe ka a dukan zamanai masu zuwa.

Karanta cikakken babi Zab 45