Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 39:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na ce, “Zan yi hankali da abin da nake yi,Don kada harshena yă sa ni zunubi,Ba zan ce kome ba sa'ad da mugaye suke kusa.”

2. Na yi shiru, ban ce kome ba,Ko a kan abin da suke da kyau!Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi,

3. Zuciyata kuwa ta cika da taraddadi,Bisa ga yawan tunanina, haka yawan wahalata zai zama,Dole ne in yi ta tambaya,

4. “Ya Ubangiji, kwana nawa zan yi a duniya?Yaushe zan mutu?Ka koya mini ranar da ajalina zai auko.

5. “Ga shi, ka gajerta yawan kwanakina!Yawan kwanakina a wurinka kamar ba kome ba ne.Hakika duk mutum mai rai,Bai fi shaƙar iska ba.

6. Bai kuma fi inuwa ba!Duk abin da yake yi banza ne,Yakan tara dukiya, amma bai san wanda zai more ta ba!

Karanta cikakken babi Zab 39