Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 39:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na ce, “Zan yi hankali da abin da nake yi,Don kada harshena yă sa ni zunubi,Ba zan ce kome ba sa'ad da mugaye suke kusa.”

2. Na yi shiru, ban ce kome ba,Ko a kan abin da suke da kyau!Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi,

3. Zuciyata kuwa ta cika da taraddadi,Bisa ga yawan tunanina, haka yawan wahalata zai zama,Dole ne in yi ta tambaya,

4. “Ya Ubangiji, kwana nawa zan yi a duniya?Yaushe zan mutu?Ka koya mini ranar da ajalina zai auko.

5. “Ga shi, ka gajerta yawan kwanakina!Yawan kwanakina a wurinka kamar ba kome ba ne.Hakika duk mutum mai rai,Bai fi shaƙar iska ba.

6. Bai kuma fi inuwa ba!Duk abin da yake yi banza ne,Yakan tara dukiya, amma bai san wanda zai more ta ba!

7. “A kan me zan sa zuciya, ya Ubangiji?A gare ka nake dogara.

8. Ka cece ni daga dukan zunubaina,Kada ka bar wawaye su yi mini ba'a.

9. Zan yi shiru, ba zan ce kome ba,Saboda ka sa na sha wahala haka.

10. Kada ka ƙara hukunta ni!Na kusa mutuwa saboda bugun da kake yi mini!

11. Kakan hukunta zunuban mutum ta wurin tsautawarka,Kamar yadda asu yake lalata abu.Hakika mutum bai fi shaƙar iska ba!

12. “Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka kuma kasa kunne ga roƙona,Kada ka yi shiru sa'ad da na yi kuka gare ka!Yadda dukan kakannina suka yi,Ni baƙonka ne na ɗan lokaci.

13. Ka ƙyale ni ko zan sami kwanciyar rai,Kafin in tafi, ai, tawa ta ƙāre.”

Karanta cikakken babi Zab 39