15. Na dogara gare ka, ya Ubangiji,Kai za ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.
16. Kada ka bar magabtana su yi murna saboda wahalata.Kada ka bar su su yi kirari a kan faɗuwata!
17. Ina gab da fāɗuwa,Ina cikin azaba kullum.
18. Na hurta zunubaina,Sun cika ni da taraddadi.