Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 35:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya,Suna hararata da ƙiyayya.

17. Sai yaushe, za ka duba, ya Ubangiji?Ka kuɓutar da ni daga farmakinsu,Ka ceci raina daga waɗannan zakoki!

18. Sa'an nan zan yi maka godiya a gaban babban taron jama'a.Zan yabe ka a gaban babban taro.

19. Kada ka bar maƙiyana, maƙaryatan nan, su ga fāɗuwata!Kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili,Su ƙyaface ni, su yi murna saboda baƙin cikina!

20. Ba su yin maganar zumunci,A maimakon haka sukan ƙaga ƙarairayi a kan masu ƙaunar limana.

21. Sukan zarge ni da kakkausan harshe,Su ce, “Mun ga abin da ka yi!”

22. Amma kai, ya Ubangiji ka ga wannan.Saboda haka kada ka ƙyale su, ya Ubangiji,Kada ka yi nisa!

23. Ka tashi, ya Ubangiji, ka kāre ni.Ya Allah ka tashi, ka bi mini hakkina.

24. Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, ka shaida rashin laifina,Kada ka bar maƙiyana su ƙyaface ni, ya Allahna!

25. Kada ka bar su su ce wa kansu,“Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!”Kada ka bar su su ce,“Mun rinjaye shi!”

26. Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata,A rinjaye su, su ruɗe.Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni,Su sha kunya da wulakanci!

27. Ka sa waɗanda suke murna da kuɓutataSu yi ta sowa ta murna, suna cewa,“Ubangiji mai girma ne!Yana murna da cin nasarar bawansa!”

28. Sa'an nan zan yi shelar adalcinka,Dukan yini kuwa zan yi ta yabonka.

Karanta cikakken babi Zab 35