Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 34:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin,Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba.

2. Zan yabe shi saboda abin da ya yi,Da ma dukan waɗanda suke da tawali'u su kasa kunne, su yi murna!

3. Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni,Mu yabi sunansa tare!

4. Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini,Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.

5. Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna,Ba za su ƙara ɓacin rai ba.

6. Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa.Ya cece su daga dukan wahalarsu.

7. Mala'ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji,Ya cece su daga hatsari.

8. Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri!Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa!

9. Ku yi tsoron Ubangiji ku jama'arsa duka,Masu tsoronsa suna da dukan abin da suke bukata.

10. Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa,Amma masu biyayya ga Ubangiji,Ba abu mai kyau da sukan rasa.

11. Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni,Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji.

Karanta cikakken babi Zab 34