Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 27:3-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ko da rundunar mayaƙa ta kewaye ni,Ba zan ji tsoro ba.Ko da magabtana sun tasar mini,Zan dogara ga Allah.

4. Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji,Abu ɗaya kaɗai nake bukata,Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji,In yi ta al'ajabin alherinsaDukan kwanakin raina,In roƙi biyarwarsa a can.

5. A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarsa,Zai kiyaye ni lafiya a Haikalinsa,Zai ɗora ni a kan dutse mai tsayi, ya kiyaye ni.

6. Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni.Da sowar farin ciki mai yawa zan miƙa sadakoki a Haikalinsa!Zan raira waƙa, in yabi Ubangiji!

7. Ka ji ni, ya Ubangiji, sa'ad da na ya yi kira gare ka!Ka yi mini jinƙai ka amsa mini!

8. Ka ce, “Zo wurina,”Zan kuwa zo gare ka, ya Ubangiji,

9. Kada ka ɓoye mini fuskarka, ya Ubangiji!Kada ka yi fushi da ni,Kada kuwa ka kori bawanka.Kai ne kake taimakona, tun dā ma,Kada ka bar ni, kada ka yashe ni,Ya Allahna, Mai Cetona!

10. Mai yiwuwa ne ubana da uwata su yashe ni,Amma Ubangiji zai lura da ni.

11. Ka koya mini abin da ya kamata in yi, ya Ubangiji,Ka bi da ni kan lafiyyiyar hanya,Domin ina da magabta da yawa.

12. Kada ka bar ni a hannun magabtana,Waɗanda suke fāɗa mini da ƙarairayi da kurari.

13. Hakika zan rayu domin in ga alherin UbangijiDa zai yi wa jama'arsa.

14. Ka dogara ga Ubangiji!Ka yi imani, kada ka karai.Ka dogara ga Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 27