Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 27:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ne haskena da cetona,Ba zan ji tsoron kowa ba.Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari,Ba zan ji tsoro ba.

2. Sa'ad da mugaye suka tasar mini,Suna ƙoƙari su kashe ni,Za su yi tuntuɓe su fāɗi.

3. Ko da rundunar mayaƙa ta kewaye ni,Ba zan ji tsoro ba.Ko da magabtana sun tasar mini,Zan dogara ga Allah.

4. Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji,Abu ɗaya kaɗai nake bukata,Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji,In yi ta al'ajabin alherinsaDukan kwanakin raina,In roƙi biyarwarsa a can.

Karanta cikakken babi Zab 27