Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 22:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sun buɗe bakinsu kamar zakoki,Suna ruri, suna ta bina a guje.

14. Ƙarfina ya ƙare,Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa.Dukan gaɓoɓina sun guggulle,Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.

15. Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura,Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama.Ka bar ni matacce cikin ƙura.

16. Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni,Suka taso mini kamar garken karnuka,Suka soke hannuwana da ƙafafuna.

17. Ana iya ganin ƙasusuwana duka.Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido.

18. Suka rarraba tufafina a tsakaninsu,Suka jefa kuri'a a kan babbar rigata.

19. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji!Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!

20. Ka cece ni daga takobi,Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.

21. Ka kuɓutar da ni daga waɗancan zakoki,Ba ni da mataimaki a gaban bijimai masu mugun hali.

22. Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi,Zan yabe ka cikin taronsu.

23. “Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji!Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu!Ku yi masa sujada, ku jama'ar Isra'ila!

24. Ba ya ƙyale matalauta,Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu,Ba ya rabuwa da su,Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”

Karanta cikakken babi Zab 22